IGC Nigeria: An Kammala Aikin Daga Darajar Yanar SupernovaAn samu nasara kammala aikin daga darajar Supernova karo na farko bayan kimanin shekara guda da wata biyu da kaddamar da shi a watan Satumban bara (2020).

Zamu duba yanda wannan daga darajar zai samar da Karin nasarori a Gamayyar Secret da kara inganta sabbin hanyoyin musanyar bayanai, wanda ai kara hade Gamayyar Secret a matsayin ta na dandalin sirri domin shiga tsarin dake kira Web3.Barkanku dai ma’abota shafin Secret!

Idan za’a iya tunawa shekara guda kenan bayan da kamfanin Secret Nertwork ya kaddamar da kwangilar kashin-kai mai kwakwalwa. Tun daga wannan lokacin tawagar dakin bincikenkamfanin Secret ke ta aiki tukuru wajen ganin an shirya samar da tsarin Supernova-wani mahimmin daga daraja da zai samar da wani dandali mai zarge da zai baiwa sirri fifikofiye da komai domin shiga tsarin Web3 da zai bude kofar samar da daruruwan abubuwa na musamman domin DeFI, NFTs, da kumasauran wasu da dama. A yau dai an sami nasarar fara anfabni da Supernova wanda zai kawo manhajar sirri zuwa Cosmos sannan kuma ya kara fito da kamfanin Secret zuwa shiga tsarin kafa harsashin Web3 metaverse.


Supernova ya samar mana da tsarin hadaka na IBC, wannan tsari shi ne a karshe ake sa ran zai hada Secret da babban dandalin hada-hada na blockchain a ilahirin muhallin Cosmos (kari kan turbar zuwa Ethereum, BSC, Monero, da kuma wasu da dama). Sannan IBC zai kara bada damar iya amfani da SCRT a zargen manhajar Cosmos (kamar Osmosis, Gravity DEX, da kuma wadanda aka gina kan tsarin Terra kamar dAppS), hakazalika kuma zai samar da sirri na musamman ga Gamayyar Secret a gaba dayan muhallin Cosmos.

Bugu da kari kuma Supernova zai kara bada damar yin wadannan abubuwa kamar haka:

- Samun har kusan ninki goma na kudin makamashi (Gas Fee)

- Hada-hada mafi sauri da kuma inganci

- Ingantacciyar gamayya da kuma Karin inagncin aiki

- Kara inganta tsare-tasren kwangila

- Tsarin Cosmos na SDK 0.44

- Hadaka da wasu gamayyar kamar Atom, Terra/Luna, Osmosis, Juno, da dai sauransu.

- Samar da tsarin Free Grand-wanda ke ba da damar shiga wani adreshi da ga wani, inda wannan zai rage wahalhalun da ake sha wajen gudanar da hada-hada.

- Rijista mai sarrafa kanta-yanzu an samar da wani umarni da zai bada damar yin rijista kai tsaye.

Kamar dai yanda za ku gani a sama, Supernova ya zo da sauye-sauye masu matukar mahimmaci da za su kara inganta da kuma saukaka daga darajar gamayyar da kuma kara bawa masana masu gina manhaja Karin damammakin shiga tsarin Gamayyar Secret na samar da manhajojin da za su mayar da hankali kan bukatun masu anfani da su. Sannan kuma Supernova ya kara bada goyon bayan samuwar hadakar asusu wanda ya ke kawo sabon tsarin hadakar kwamfita da ake kira CosmWasm wand zai inganta yanda kwamfitoci za su dinga aikin su tare wajen musayar bayanai.

Har ila yau aikin daga darajar Supernova ya zo da abubuwa kamar: sabbin manhajojin Secret da aka kaddamar a karamin dandalin su na yanar gizo-gizo da ake kira mainnet, samun Karin sabbin abokan hurda da kuma na hadin gwuiwa, sannan kuma da miliyoyin sabbin damammaki ga masu anfani da shafin da kuma magina manhaja.


10 views0 comments