IGC Nigeria:Quentin Tarantino Zai Baje Kolin Pulp Fiction a Kasuwar NFTHoton mashiryin fina-finai Quentin Tarantino tsaye kusada pastar fim din ‘Pulp Fiction’ a Birnin Landan a shekarar 19194


Quentin Tarantino ya shigo harkar NFT gadan-gadan


Babban daraktan da ya lashe manyan kyautuka ya bayyana cewa zai bada kyautar wasu fitar dabe guda bakwai daga cikin shirin fim din ‘Pulp Fiction’ a matsayin gwanjo na NFT. A ranar Talatar da ta gabata ne wato 2/11/2021 babban daraktan ya bayyana hakan. Za kuma a hada da rubutun labarin shirin fim din na ainihi da kuma kundin murya na sharhin da shi darakta Quentin din yayi da kansa. Za’a sanya wannan kadara ne a shafin gwanjon Tukuicin NFT mai suna OpenSea.


NFT dai ko Non-fungible Token a Turance na nufin wasu abubuwa ma su cike da tsaro wadanda akan gina akan shafukan hada-hadar sulallan yanar gizo-gizo da ake kira Gamayyar Sirri (Secret Network) wadda wani tsari ne a farfajiyar crypto ta blockchain inda akafi bawa sirri matukar mahimmanci a cikin su fiye da komai. Wanann na nufin samar tsarin NFT na musamman ga ‘Pulp Fiction’ da kuma sauran gwanjon da aka dora a wannan kafar, kuma dole ne ya zamana mamallaka NFT din ne kadai ke iya ganin abubuwan da ke ciki.

Gammayyar Sirri kon kuma Secret Network a Turance itace ta farko a tsarin blockchain da ke da tsarin adana sirri mai kwakwalwa wato privacy-preserving smart contracts a Turance. Wannan na nufin cewa duk wata hada-hada da mallakar bayanai na cikin tsarin garkamewa na sirri da ake kira encryption.


Abinda da yake bisa al’ada a baya shi ne duk wata hada-hada da kuma mallakar bayanai a bude su ke hanhai ga jama’a a tsarin sauran NFT da aka gina akan wasu shafuikan blockchian kamar Ethereum. Wannan ya zama kamar ga koshi ga kuma kwanan yunwa. Saboda barin sa a bude a shafukan blockchain na bada damar tantance hada-hada, saidai kuma ya na bada damar iya bin diddigin kowace hada-hadar da aka gudanar duk da sunayen giri da hotunan gangan da ake yawan anfani da su a tsarin crypto.

Manyan masu saka hannun jari a kamfanin A16z, Katie Haun da kuma Ali Yahya sun bayyana wannan rashin sirrin na blockchain a matsayin daya da ga cikin abubuwan da ke kawo koma-baya ga Kwangila mai Kwakwalwa wato smart contracts. A wani rubutu da a ka wallafa a farkon shekarar nan shafin Aleo wani, shafin hada-hadar sulallan yanar gizo-gizo ya bayyana cewa: “Ana bukatar Wannan tarnakin ne domin akwai bukatar tantancewa kafin a amince da duk wata hada-hada. Ita dai hada-hadar kudade a blockchain na bukatar a bar su a bude saboda kowa da kowa ya iya tantance cewa daidai su ke.”


Tsarin zero-knowledge na Aleo ya tabbatar da cewa masu gudanar da cryto na yunkurin cire wadannan tarnakai sannan kuma kamfanin Galaxy Digital da kuma Coinbase Ventures sun bada hasashe kan hakan inda su ka shiga cikin tsarin samar da kudade kamar kamfanin A16z, babban kamfanin zuba jarin crypto da Marc Andreessen da kuma Ben Horowitz su ka kafa.


Sulalla masu sirri ko kuma privacy coins a Turance akan kirkire su ne da kadarori kamar su Monero, Zeash, verge, da wasun su da ke baiwa masu anfani da su Karin matakan sirri ga kadarorin su wanda sauran tsare-tsare na blockchain kamar Bitcoin masu adana bayanan hada-hada a bainar jama’a sam ba su da su kwata-kwata.

Tsarin Gamayyar Sirri wato Secret Network da kuma Sectet NFT na iya daukan bayanan sirri da kuma budaddu duk a lokaci guda. Wannan wata manhaja ce ta sirri ta musamman da kamfanin ke da yakinin zata sauya al’amura da dama kamar hotunan sirri, abubuwan da aka tanada domin baligai, kebantattun bayanai ko kuma na biya, tsarin siyan tikiti, da kuma katin shaida da kuma paspot.

Kamar dai yanda sulalla masu sirri su ke kare sirrin masu anfani da su, hakazalika su ma NFT ke kare hakkin masu zane-zane da masu tattara bayanai, matukar sun zabi yin hakan. Yayin kare bayanan jam’a da kuma na hada-hadar su ke kara matso da fasahar blockchain kusa ga kudade da kuma tsarin hada-hadar kudade na gargajiya, to akwai kuma bukatar kara inganta sirri a tsarin da daman yake da sirri. Hausawa na cewa: “Ko kana da kyau ka kara da wanka.” Wannnan zai kara tsananta sanya ido daga masu lura. Hankalin manyan kamfanoni kamar IRS sun koma kan kamfanin Manero yayinda wata hukumar gwamnati ta bada ladan dalar Amurka 625,000 ga wasu yan kwangila domin bin diddigin wasu hada-hada a shekarar 2020.


Bawai iya masu shirya fina-finaI tsarin Tarantino na NFT mai sirri yake karewa ba a sashen film din Pulp Fiction, wanda ba’a yiwa editin ba, amma harda bayanan sirri na wadanda za su mallaka a karshe. Wannan shi ne abinda ake yayi a tsarin canke na NFT a masana’antar shirya fina-finai ta Hollyhood a halin yanzu, biyo bayan hadin gwuiwar NFT na shahararren mai shirya fina-finan nan wato David Lynch da kuma hukumar yan sandan kasa-da-kasa a watan da ya gabata.

Hakazalika kamfanin shirya fina-finai na MGM ya shiga wani hadin gwuiwa da kamfanin Veve domin gabatar da tsarin tukuicin NFT a shahararren film din nan mai suna “No Time to Die” inda haka ya mai da shi fim din shahararen darakta James Bond na farko da zai shiga tsarin tattara kayan fasaha na zamani.


Yayinda yake kaddamar da tsarin, mista Tarantino ya fadawa magoya bayan sa cewa: “Ina mai matukar farincikin gabatar muku da wasu bangarori a cikin shirin fim din Pulp ‘Fiction’. Ya kuma kara da cewa: “Gamayyar Sirri wato (Secret Network) da kuma NFT na Sirri (Secret NFT) sun samar da wata irin sabuwar duniya da ke hada masoya da kuma taurarin fina-finaI, kuma ina mai matukar zumundin murnar kasancewa ta daya daga ckin su.”

Ana sa ran mista Tarantino zai gabatar da sharhi kan fim din NFT na ‘Pulp Fiction’ tareda shahararren mai zuba hannun jari a hada-hadar sulallan yanar gizo-gizo kuma wanda ya kafa, kuma mamallakin (CEO) kamfanin Galaxy Digital wato mista MIKE Novogratz da sauran wasun su a babban taron karawa juna ilimi na NFT NYC a yammacin ranar Talatar da ta gabata.
Shirin fim din Tarantino na ‘Pulp Fiction’ shi ne shirin sa na biyu wanda ya fita kimanin shekaru 27 da su ka gabata wato a shekarar 1994. Shirin ya girgiza duniyar fina-finai ta wancan zamanin sannan kuma ya kara bunkasa kamfanin shirya fina-finai na Miramax wanda yan uwan nan su biyu suka kafa wato Bob Weinstein da kuma dan uwansa Harvey Weinstein, wanda a halin yanzu aka kama da laifin badalar zina. Shirin fim din ‘Pulp Fiction’ sai da ya lashe kyautar Palme D’Or, kyauta mafi girma a Cannes a shekarar 1994. Sannan kuma Mista Tarantino da mataimakin mai rubutuwa, kuma mashiryin fina-finan nan dan kasar Kanada, mista Roger Avery sun sake lashe babbar kyautar Oska a shekarar 1995. Hakika shirin fim din ‘Pulp Fiction’ ya mayar da Samuel L. Jacson wani babban tauraro yayinda kuma ya sake farfado da tauraruwar John Travolta bayan da fim din ya fita.11 views0 comments